BREAKING NEWS :- MASU GARKUWA DA MUTANE SUKAI KARA HUKUMAR YANSANDA KAN HANASU KUDIN FANSAR SU || bakinganga.blogspot.com
Mai garkuwa da mutane ya ƙi amincewa da kaso dubu N200,000 cikin miliyan 12 da aka bashi na kuɗin fansa, wanda har hakan yasa ya kai rahoto ga ƴan sanda.
Wani mutum a jihar Adamawa ya bayyana cewa shi dan ƙungiyar masu garkuwa da mutane ne, waɗanda suka karɓi kuɗin fansa naira miliyan 12 daga hannun wasu mutane biyu da aka kashe
Sadu Bunkawu sheda wa ƴan sanda cewa ya samu saɓani ne da ƴan ƙungiyarsa bayan sun ba shi Naira 200,000 kacal daga cikin Naira miliyan 12 da suka samu a aikin da suka yi na ƙarshe, kamar yadda The Nation ta rawaito.
Da yake bayyana kason nasa da cewa kuɗin da aka bashi sun yi kaɗan, sai ya kai ƙarar abokan aikin nashi ga ƴan sanda domin su bi masa haƙƙinsa na rashin adalcin da aka masa.
Bunkawu mai shekaru 28 a ƙauyen Filingo da ke ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa ya bayyana cewa an biya su kuɗin fansa N12m a lokacin da suka yi garkuwa da Umaru Diffiwa da Umaru Babidi ƴan unguwa ɗaya.
Ya kuma bayyana nadama a kan cewa lallai aikin ya yi masa illa domin hatta Naira 200,000 da ya karɓa ya faɗi a hanyarsa ta komawa gida.
Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da Sadu Bunkawu a gaban babbar kotun majistare 1 da ke Yola bisa zargin haɗa baki da kuma yin garkuwa da mutane. Lokacin da aka karanta ma sa rahoton bayanin Farko kuma aka fassara masa a gaban kotu, ya amsa laifinsa.
Bayan kammala ƙarar, ɗan sanda mai shigar da ƙara ya roƙi kotun da ta ɗage shari’ar don ba shi damar kammala bincike tare da kai takardar ƙarar zuwa sashin shari’a don neman shawarar lauya. Alƙalin kotun, Muhammad Abdullahi, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa wata mai zuwa, 4 ga Afrilu.
✍️Miskidor
Comments
Post a Comment