News :- APC TA BADA MUKAMIN SHGABANCI... || bakinganga.blogspot.com

 



APC ta bai wa yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya muƙamin shugaban jam'iyya

Kwamatin shugancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ƙasa ya bayyana muƙamai da ya ware wa kowane ɓangaren siyasar ƙasar kafin babban taronta na ƙasa ranar 26 ga watan Maris.

Cikin wata sanarwa, APC ta bai wa ɓangaren arewa ta tsakiya muƙamin shugaban jam'iyya, yayin da kudu maso yamma zai samar da sakatare.

An bai wa yankin kudu maso gabas muƙamin mataimakin shugaban jam'iyya.

Ta ce an cimma matakin rarraba muƙaman ne a zaman da kwamatin ya yi ranar Talata.

Sanarwar ta biyo bayan sabuwar dambarwar da ɓarke ne na shugabancin jam'iyyar a shekaranjiya bayan da gwamnan Neja ya karbi ragamar daga hannun gwamnan Yobe.


✍️ Miskidor

Comments