News :- BABBAN DALILIN DAYASA AKE WAHALAN MAI A NIGERIA || bakinganga.blogspot.com

 


Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu wato IPMAN ta musanta cewa ɓoye man fetur da ake zargin wasu dillalai ke yi shi ne ya ƙara ta'azzara ƙarancin man fetur da ake yi a Najeriya. 

Shugaban ƙungiyar IPMAN shiyyar arewa maso yammacin ƙasar Alhaji Salisu 10-10 ne ya musanta hakan a yayin wata hira da BBC inda ya ce mambobin ƙungiyar na iyakacin ƙokarinsu don ganin an kawo ƙarshen ƙarancin man fetur da ake fuskanta.

An shafe makonni ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a jihohi da dama na Najeriya, lamarin da ya haddasa wahalhalu ga masu ababen hawa baya ga ƙaruwar farashin sufuri.

A cewar Alhaji Salisu, ya ce ba ya tunanin akwai wani dillali mai gidan mai da zai ɓoye mai domin mutane su wahala.

"A matsayinka na ɗan kasuwa mai gidan mai kuma mai zaman kansa za ka je ka cire kuɗinka ka sawo mai ka zuba domin ka sayar wa al'umma a ce kuma za ka boye, to idan ka ɓoye ka yi me da shi?" in ji Alhaji Salisu.



Ya kuma musanta zargin da ake yi cewa dillalan man kan saye mai su ajiye idan aka yi ƙarancinsa sai su tsauwala farashi.

Alhaji Salisu ya kuma yaba wa kamfanin mai na Najeriya wato NNPC inda ya ce yana iya bakin ƙoƙarinsa wurin samar da mai a Najeriya amma ya ce matsalar da ake samu a halin yanzu wadda ke ƙara ta'azzara wahalar mai ita ce ƙarancin man dizal.

Ya ce motocin da za su je su ɗauko musu mai a Legas da Warri da Fatakwal da Calabar akasarinsu ba su iya zuwa saboda ƙarancin dizal ɗin da za su zuba musu.

Ya ce ƙoƙarin da NNPC take a yanzu shi ne tana ba wasu ƴan kasuwar da ta yarda da su isashen man dizal su zuba a motocinsu domin su je su yi lodi su dawo.



A kwanakin baya ne dai matsalar ƙarancin mai a Najeriya ta ƙara ta'azzara tun bayan wani gurɓataccen mai da aka shiga da shi ƙasar.

Gurbataccen man ya jawo asarar biliyoyin nairori inda har motocin mutane suka rinƙa lalacewa sakamakon man da suka sha.



Hakan ya jawo tsaiko da katsewar mai a gidajen mai wanda sai daga baya kamfanin NNPC ya sanar da shigo da sabon man fetur mai inganci ƙasar wanda ya ce tuni aka fara rarraba shi

✍️Miskidor

Comments