NEWS :- KUNGIYAR ASUU TA TSAWAITA WA'ADIN YAJIN AIKINTA ZUWA MAKWANNI 8 || bakinganga.blogspot.com

 Kungiyar malaman jami'o'in ta Najeriya, ASUU, ta sanar da tsawaita wa'adin yajin aikin da suka tafi zuwa makwanni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar.

Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau jami'i ne a kungiyar ta ASUU, ya ce sun dauki matakin kara wa'adin ne domin bai wa gwamnati damar cimma sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun kara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.



Ya ce makwanni 8 sun wadatar matukar gwamnatin da gaske take kan daukar matakin da ya dace.



Tattaunawa da Farfesa Abdulkadir kan yajin aikin ASUU

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron tattaunawar Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau tare da Badriyya Tijjani Kalarawi.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.

Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

Abin da shugabannin jami'o'i suka ce

Ƙungiyar shugabannin jami'o'in tarayya wato Committee of Vice Chancellors of Nigerian Universities ta ce jami'o'in ƙasar ba za su jurewa tsawaita yajin aikin malaman jami'a ba.

Ƙungiyar shugabannin jami'o'i ta ce sai gwamnatin tarayya ta tashi tsaye don gudun jefa ilmin jami'a cikin halin ni-'ya-su.

Farfesa Yakubu Aboki Ochefu shi ne sakataren ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya kuma ya ce wa BBC maganar ASUU da gwamnatin tarayya ya kamata a shirya saboda shekara fiye da 30 kenan aka fara wannan batun.

"Idan sun tattauna mafi tsayi shi ne a yi shekara biyu ko uku sai ka ji an fara wani yajin aikin kuma. Mene ne yake faruwa?

"Yarjejeniyar ce gwamnatin tarayya ba ta iya cikawa ko me? Abin takaicin dai shi ne ɗalibai ne suka fi shan wahala a cikin wannan faɗa na ASUU da gwmantai.

Ya ƙara da cewa komai ya ta'allaƙa a kan gwamnati, sannan ya taɓo batun yanayin da jami'o'in ke ciki da ke shafar ɗaliban kamar cunkoso a ajujuwa da kuma rashin isassun malamai.

Farfesa Yakubu ya ce yana fargabar idan har ba a daidata tsakanin gwamnati da ASUU ba to ba za a koma makarantu ba, ɗalibai za su yi rashin karatu.

"Kuma ƴƴn talakawa ne wannan lamarin zai fi shafa," in ji shi.





Comments